‘Yan Aware A Yankin Arewa Maso Yammacin Kasar Kamaru Sun Yi Garkuwa Da Mata Sama Da 30

0 108

‘Yan aware a yankin arewa maso yammacin kasar Kamaru sun yi garkuwa da mata sama da 30 tare da jikkata wasu da ba a tantance adadinsu ba.

Jami’ai sun ce an sace matan ne a wani kauye mai suna Big Babanki da ke kusa da kan iyaka da Najeriya, bisa zargin nuna adawa da dokar hana fita da kuma haraji da ‘yan awaren suka kakaba musu.

Wasu kafafen yada labarai na kasar sun rawaito cewa adadin wadanda aka sacen ya fi haka, kimanin mata 50 ne.

Jami’ai sun ce ‘yan tawayen da ke dauke da muggan makamai sun azabtar da wasu matan, wadanda sukan yi garkuwa da fararen hula, akasari domin neman kudin fansa.

Shugaban ‘yan awaren, Capo Daniel, ya shaida wa manema labarai cewa, ana hukunta matan ne saboda yadda gwamnatin Kamaru ta ke amfani da su.

Rundunar sojin ta ce ta tura dakaru domin kubutar da matan. Kasar Kamaru dai na fama da fadace-fadace tun a shekarar 2017 da ‘yan aware masu amfani da yaren Ingilishi suka kaddamar da tawaye.

Leave a Reply

%d bloggers like this: