Wasu maniyyatan da za su je aikin Hajji a jirgin farko sun yi hatsari a hanya

0 131

Motar maniyyatan ta yi hatsari ne a ranar Laraba a kan hanyarsu ta zuwa Abuja inda za su hau jirgin farko a ranar Alhamis.

Maniyyatan aikin Hajjin bana daga Jihar Nasarawa da ke shirin tafiya a jirgin farko sun yi hatsari.

Rahotanni sun nuna mutum hudu sun samu rauni bayan motar maniyyatan ta yi adungure da su ne a ranar Laraba a kan hanyarsu ta zuwa Abuja inda za su hau farko a ranar Alhamis.

Hatsarin da ya ritsa da bas mai daukar mutum 18 da suke ciki ne a yankin Kara da ke Karamar Hukumar Keffi a Jihar Nasarawa kamar yadda Aminiya suka wallafa.

Leave a Reply

%d bloggers like this: