RFEF Ta Rufe Filin Wasa Na Valencia Ta Kuma Caje Su €45,000

0 145

An tilastawa Valancia ta rufe gurbin kallon wasa na Mario Kempes na tsawon wasanni biyar da kuma su biya tarar Yuro 45,000 bayan da hukumar kwallon kafa ta kasar Spain ta samu magoya bayan kungiyar kwallon kafa na Valancia da cin zarafin Vinicius Jr a wasan da suka buga da Real Madrid a ranar Lahadi;
Wajen tsayawa na Mario Kempes, inda waken cin fuska da aka yiwa Vinicius ta samo asali a wasan da Valencia ta ci 1-0 ranar Lahadi, za a rufe shi a wasanni da Valencia zata fafata a gida, wasa daya da ya rage a mata a gida wannan kakar da kuma wasanni hudu na farko na kakar wasa mai zuwa.
A cikin wata sanarwa da ta fitar, RFEF ta ce: “Kwamitin gasar ta hukunta Valencia CF da rufe wani bangare na filin wasa na Mestalla na wasanni biyar, musamman ma bangare kudu na Mario Kempes, biyo bayan abubuwan da suka faru a wasan da fafata da kungiyar Real Madrid.
“An yi la’akari da cewa, kamar yadda alkalin wasa ya nuna a cikin rahotonsa, an yi ihun wariyar launin fata ga Vinicius, wanda ya canza yanayin wasan da ake bugawa, kuma an dauki laifuffukan da muhimmanci.
“Bugu da ƙari, an sanya takunkumin tattalin arziki na € 45,000 akan Valencia.
Sun kara da cewa: “Kwamitin gasa na RFEF ya yi la’akari da cewa tantancewar da alkalin wasa ya yi shi ne bisa watsi da wani bangaren wasan da aka yi, wanda ya shafi hukuncin alkalin wasa.
“a gaskiyar lamari, an hana shi wani muhimmin bangare na gaskiyar lamarin ya sa ya yanke hukunci na son rai. Kuma hakan ya faru ne saboda rashin tantance abin da ya faru yadda ya kamata.”
A cikin cikakken rahotonta, RFEF ta gano cewa an tabbatar da cewa Vinicius yana fuskantar cin zarafi na wariyar launin fata ne lokacin da motar Real Madrid ta fara isa Mestalla.
A yayin wasan yake gudana, an jefa masa abubuwa a daidai minti na 71 daga Kempes Stand, kafin daga bisani aka rika rera wakar wariyar launin fata a daidai minti na 73 – lokacin da alkalin wasa ya sanar da wakilin wasan da yayi sanarwa a PA.

Leave a Reply

%d bloggers like this: