Rundunar ‘Yan Sandan Jihar Jigawa Sun Tarwatsa Wani Gungun Barayi A Birnin Dutse

0 107

Jami’an rundunar ‘yansandan jihar Jigawa sun tarwatsa wani gungun barayi dake addabar rukunin gidajen Inuwa Dutse a Danmasara, Dutse.
Kakakin rundunar ‘yansandan jiha, Lawan Shiisu Adam, wanda ya tabbatar da kamen yace yazo ne sanadiyyar salon yaki da masu aikata laifi wanda rundunar ta fara amfani da shi, a wani bangare na tabbatar da cewa an samu zaman lafiya a jihar.
A cewarsa, ‘yansandan sun kama wani mutum dan shekara 27 mai suna Ibrahim Abdullahi na unguwar Na’ibawa a jihar Kano, dauke da wani babur na sata samfurin Jincheng.
Yace an kuma kama wasu mutane hudu da ake zargi da suka hada da Hassan Aliyu dan shekara 18 da Zakar Mohammed mai shekaru 27 da Uzairu Mohammed mai shekaru 28, dukkansu a yankin karamar hukumar Hadejia bisa laifin karbar kayan sata.
Shiisu Adam yace bincike ya kai ga kwato kayayyakin sata da dama da suka hada da filasma talabijin mai fadin inci 58 da wata fanka da ake yiwa chaji da kafet guda 2 da jakar bulaguro 1 da zanin gado 1 da huluna 2 da kaya kwat kala 1 da riga t-shirt guda 1.

Leave a Reply

%d bloggers like this: