Majalisar Zartarwa Ta Amince Da Aikin Wutar Lantarki A Masarautar Daura Kan Naira Biliyan 4

0 97

Majalisar Zartarwa ta Tarayya a jiya ta amince da kwangilolin da za su habaka samar da wutar lantarki a sassan kasarnan da dama.

A cewar ministan wutar lantarki, Abubakar Aliyu, kwangilolin sun hada samarwa da kafa kayan aikin karamar tashar wutar lantarki mai karfin kilo voltage 33 a masarautar Daura ta jihar Katsina, wacce aka bawa kamfanin Power Deal akan kudi naira miliyan dubu 4.

Ministan yace an kuma amince da kwangilar daga likkafar karamar tashar wutar lantarki a garin Potiskum na jihar Yobe wacce za ta sanya mata tiransfoma guda 132.

Abubakar Aliyu yace an amince da kudi dala miliyan 6 na kayan da za a sayo daga waje da naira miliyan 145 na kayan da za a saya a cikin kasa domin samar da kayayyakin watsa wutar lantarki ga kamfanin watsa wutar lantarki na kasa (TCN). Majalisar ta kuma amince da kudade dala miliyan 61 da dubu 500 da kuma naira miliyan dubu 16 da miliyan 733 da dubu 500 domin sayo kayan aikin watsa wutar lantarki.

Leave a Reply

%d bloggers like this: