‘Yan Najeriya Za Su Iya Neman Bankunansu Su Basu Katin ATM Mai Hade Da Katin Dan Kasa

0 81

Gwamnatin tarayya tace daga yanzu ‘yan Najeriya za su iya neman bankunansu su basu katin ATM wanda zai kuma yi aiki a matsayin katin dan kasa ba tare da karin kudi ba.

Ministan sadarwa da tattalin arzikin dijital, Isa Pantami, wanda ya sanar da haka jiya a Abuja, yace an samu amincewar yayin zaman ganawar majalisar zartarwa ta kasa.

Yayi bayanin cewa amincewar ta biyo bayan wata takardar bukata daga hukumar shaidar zama dan kasa dake neman barin bankuna su fitar da katin mai amfani daban-daban wanda zai yi a matsayin katin dan kasa.

A wani batun kuma, karamin ministan kwadago da samar da aikin yi mai baring ado, Festus Keyamo, ya nemi a soke mukamin karamin minista a majalisar tarayya, inda yace sabawa dokar kasa ne a nada karamin minista. Festus Keyamo ya sanar da hakan jiya yayin zaman ganawar majalisar zartarwa ta tarayya da aka gudanar a dakin taro na fadar shugaban kasa dake Abuja.

Leave a Reply

%d bloggers like this: