Gwamnatin Tarayya Ta Saka Kudi N1.5Bn A Asusun Banki Domin Samar Da Jari Ga Tsaffin Tsagerun Neja Delta

0 73

Gwamnatin Tarayya ta saka kudi naira miliyan dubu 1 da miliyan 500 a asusun banki domin wani shirin samar da jari da aka kaddamar domin tsaffin tsagerun Neja Delta.

Kantoman shirin afuwa ga tsagerun na shugaban kasa, Barry Ndiomu, shine ya kaddamar da shirin jiya a Abuja.

Yayi bayanin cewa an samar da kudaden domin tsaffin tsagerun su samu kafa sana’o’in da suke bukata wadanda za su mayar da su masu dogaro da kawunansu.

Yace an tsara hakan ne domin rage dogaron da suke yi da tallafin naira dubu 65 da ake bawa kowannensu a kowane wata.

Barry Ndiomu yace kudaden wadanda aka ajiye a bankin Providus, zai kasance na kaddamar da shirin, yayin da ofishinsa yayi aniyar tallafawa shirin da naira miliyan 500 kowane wata.

An nada tsohon alkalin kotun koli kuma wakili a majalisar shari’ah ta kasa, Francis Tabai, a matsayin shugaban kwamitin shura wanda zai kula da shirin samar da jarin.

Leave a Reply

%d bloggers like this: