Gwamna Badaru Ya Jinjina Wa Gwamnan Katsina Wajen Aiwatar Da Ayyukan Raya Kasa

0 81

Gwamnan jihar Jigawa Muhammad Badaru Abubakar ya jinjiniwa takwaransa na jihar Katsina Alhaji Aminu Bello Masari wajen aiwatar da ayyukan raya kasa ga al ummar jihar.

Gwamna Badaru ya bayyana hakan ne a lokacin kaddamar da rukunin gidaje 182 a Unguwar Yan Daka dake birnin Katsina.

Yace gidajen zasu rage karancin mahalli a tsakanin ma’aikatan jihar da suke aiki dana gwamnatin tarayya da ake turawa jihar.

A nasa jawabin Gwamna Aminu Bello Masari ya godewa Gwamna Badaru Abubakar da yan tawagarsa bisa amsa gayyatar kaddamar da sabbin gidajen.

A jawabinsa na maraba, Janar Manajan hukumar gidaje ta jihar Katsina, Auwal Abubakar Masari, yace an gina gidajen akan kudi naira miliyan dubu 2 da miliyan 800. Ya kara da cewa an samarwa da rukunin gidajen hanyoyi da magudanan ruwa da ruwan sha da kuma kayayyakin more rayuwa.

Leave a Reply

%d bloggers like this: