Hukumar Jin Dadin Alhazai Ta Jihar Jigawa Ta Nuna Alhini Bisa Ragin Kudin Guzurin Maniyyata

0 75

Hukumar Jin dadin Alhazai ta Jihar Jigawa ta nuna alhini bisa ragin kudin guzurin maniyyata na Dala 100 da aka samu a bana daga hukumar kula da aikin Hajji ta kasa.

Sakataren Zartarwa na hukumar, Alhaji Ahmed Umar Labbo ya bayyana haka a wata ganawa da manema labarai a Dutse.

Ahmed Umar Labbo ya ce tuni hukumar ta aike da kudin guzurin maniyyatan ta kashin farko ga banki domin daukar matakin da ya dace.

Ya bukaci maniyyata da su tabbatar sun yi amfana da abubuwan da suka koya a lokacin bita domin samun saukin gudanar da aikin Hajji ingantacce. Sakataren Zartarwar ya godewa Gwamna Muhammad Badaru Abubakar bisa irin gudummawar da yake baiwa hukumar a matakai daban-daban domin samun nasarar aikin Hajji.

Leave a Reply

%d bloggers like this: