Majalisar Karamar Hukumar Auyo Tare Da Hadin Gwiwar Wasu Kungiyoyi Sun Yashe Magudanan Ruwa A Garin Auyo

0 87

Majalisar karamar hukumar Auyo a jihar Jigawa tare da hadin gwiwar kungiyoyin aikin gayya sun yashe magudanan ruwa a garin Auyo da nufin magance cututtuka da dakile ambaliyar ruwa.

Shugaban sashen ruwa da tsaftar jiki na karamar hukumar, Alhaji Abdulmutallib Babale, shine ya sanar da haka bayan aikin gayyar na kwanaki 3 da sashen ya shirya.

Ya nanata jajircewar karamar hukumar wajen tallafawa kungoyoyin aikin gayya suke gudanar da tsaftar muhalli.

Abdulmutallib Babale ya yabawa gwamnatin jiha da ta karamar hukumar bisa inganta harkokin kiwon lafiya. Yayi kira ga magidanta da su dabbaka tsaftar muhalli da ta jiki a gidajensu da unguwanninsu.

Leave a Reply

%d bloggers like this: