An Yanke Wa Wani Mutum Hukuncin Daurin Wata 6 A Gidan Kaso Bisa Kwace Wayar Makociyarsa

0 50

Wata kotun shari’ah a jihar Kano dake zamanta a Kwana Hudu ta yanke hukuncin daurin wata 6 a gidan kaso ga wani mutum mai suna Naziru Abubakar bisa kwace wayar makociyarsa ta jefar da ita a kasa.

Alkalin kotun, Nura Yusuf Ahmad, ya kuma yanke hukuncin cewa za a yiwa mai laifin bulala 30.

Tunda farko, an gurfanar da Naziru Abubakar bisa laifin kwace wayoyin hannu biyu da kudinsu ya kai naira dubu 80 daga wata matar aure tare da jefar da ita a kasa a kauyen Gayawa dake karamar hukumar Ungogo.

Lokacin da lauya mai gabatar da kara, Aliyul Abidin, ya karanta masa laifukan da ake tuhumarsa, ya amsa laifinsa.

Lauyan mai gabatar da kara ya kuma roki kotun da ta yanke hukuncinta bisa la’akari da sashe na 350 na kundin manyan laifuffuka.

Alkali Yusuf Ahmad, baya ga daurin wata 6 a gidan kasa ba tare da zabin biyan tara ba, da kuma bulala 30, ya kuma umarci mai laifin ya biya kudi naira dubu 50 na daya daga cikin wayoyin.

Leave a Reply

%d bloggers like this: