‘Yan Bindiga A Jiya Sun Kashe Jami’an ‘Yansanda 3 A Jihar Ebonyi

0 68

‘Yan bindiga a jiya sun kashe jami’an ‘yansanda 3 dake aiki a ofishin ‘yansanda na Oshiri dake yankin karamar Onicha a jihar Ebonyi.

An gano cewa lamarin ya auku da misalin karfe 8 na safe a jiya.

Hakan yazo ne kasa da awanni 40 bayan an kashe wani sufeton ‘yansanda dake aiki a helkwatar ‘yansandan jihar Ebonyi a ranar Litinin.

‘Yan bindiga sun harbi marigayin sufeton yayin da yake aikin binciken ababen hawa a kusa da shatale-talen Union bank a babban birnin jihar.

An kuma raunata abokan aikinsa biyu a harin wadanda ‘yan bindigar suka kaddamar akan keke napep. Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yansandan jihar wanda ya tabbatar da aukuwar hare-haren yace ‘yansandan rundunar sun kashe biyu daga cikin ‘yan bindigar da suka kashe ‘yansanda uku a Oshiri.

Leave a Reply

%d bloggers like this: