Asusun Lamuni Na Duniya (IMF) Ya Amince Da Yarjejeniyar Bashin $3.5Bn Da Kasar Ivory Coast

0 79

Asusun lamuni na duniya (IMF) ya amince da yarjejeniyar bashin dala miliyan dubu 3 da miliyan 500 da kasar Ivory Coast, wanda yace za ayi amfani da bashin wajen dakile kalubalen kudi da tallafawa farfadowar tattalin arzikin.

Kasar za ta samu kimanin dala miliyan 500 ba tare da bata lokaci ba.

Sauran kudaden za su Dogara ne akan yadda kasar ta Ivory Coast ta sauya tattalin arzikinta.

Asusun na IMF yace bashin zai taimakawa kasar dakile kalubale uku da suka jawo matsaloli na annobar corona da matsin kudaden duniya da kuma mamayar da Rasha ta yiwa Ukraine.

A wani labarin na Afrika, ana gudanar da zabe a larduna 30 na jihar Puntland dake arewa maso gabashin Somalia wacce take da kwarya-kwaryar ‘yancin cin gashin kai. Sai dai, ana nuna damuwa akan yanayin tsaro saboda rikici tsakanin shugaban yankin Putland, Sa’id Abdullahi Deni, da masu adawa da shi a siyasance wadanda ke zarginsa da shirye-shiryen kara wa’adin mulkinsa.

Leave a Reply

%d bloggers like this: