Lambar Girma Ta GCON Da Aka Bani Ta Saka Ni Kankan Da Kai

0 87

Mataimakin shugaban kasa mai jiran gado, Kashim Shettima, ya ce karramawar da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yi masa da lambar girmamawa ta kasa ta GCON, abu ne da ya sanya shi kankan da kai.

Kashim Shettima ya zanta da manema labarai na fadar shugaban kasa bayan wata ziyarar ban girma da ya kaiwa mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo a jiya a fadar shugaban kasa dake Abuja.

Tunda farko a jiyan, Kashim Shettima tare da zababben shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu, sun kasance a dakin taro na fadar shugaban kasa, inda shugaban mai barin gado ya karrama su da lambobin girmamawa na kasa.

An karrama Bola Ahmed Tinubu da lambar girmamawa ta kasa ta GCFR, yayin da Kashim Shettima ya samu lambar girmamawa ta GCON. Zababben mataimakin shugaban kasar ya bayyana cewa gwamnatin mai jiran gado ta Bola Ahmed Tinubu za ta taka rawar gani ba tare da bata lokaci ba, da zarar an rantsar da ta.

Leave a Reply

%d bloggers like this: