Ina Daya Daga Cikin ‘Yan Jarida Mafiya Fushi A Kasarnan A Lokacin Da Aka Nada Ni Minista – Adamu Adamu

0 76

Ministan Ilimi, Adamu Adamu ya ce yana daya daga cikin ‘yan jarida mafiya fushi a kasarnan a lokacin da aka nada shi ministan ilimi.

Ministan ya bayyana haka ne a wajen wani taron karramawa da ma’aikatarsa ta shirya domin karrama shi da na karamin ministan ilimi, Goodluck Opiah, jiya a Abuja.

Adamu Adamu ya ce saboda tsaurin ra’ayinsa, yana ganin bai dace kowane Shugaban kasa ya nada shi minista ba.

Ministan ya yaba da kundin dabarun ministoci a matsayin kayan aikinsa da tsare-tsarensa a cikin shekaru 8 da yayi yana mulki.

Ministan wanda ya godewa Allah (SWT) da kuma shugaban kasa Muhammadu Buhari bisa damar da aka ba shi na yiwa kasa hidima, ya ce shugaba Buhari ya dade yana taimaka masa.

Ya kuma godewa manyan sakatarorin da suka yi aiki tare da shi, ciki har da shugabar ma’aikata ta tarayya, Folashade Yemi-Esan, kan rawar da ta taka wajen aiwatar da kundin dabarun ministoci.

Leave a Reply

%d bloggers like this: