Yunkurin Da Shugaba Buhari Yayi Na Yaki Da Cin Hanci Da Rashawa Abin A Yaba Ne

0 79

Shugaban Hukumar Yaki da yi wa Tattalin Arzikin Kasa Ta’annati, EFCC, Abdulrasheed Bawa, ya bayyana yunkurin Shugaba Muhammadu Buhari na yaki da cin hanci da rashawa a cikin shekaru takwas da ya yi yana mulki a matsayin abun a yaba.

Abdulrasheed Bawa ya bayyana haka ne a jiya a wata hira da manema labarai a wajen bikin yaye sabbin ma’aikatan hukumar EFCC da aka horas a kwalejin horar da rundunar ‘yan sandan mobayil da ke Ende Hills a Akwanga, jihar Nasarawa.

Sabbin ma’aikatan su 115 sun kunshi maza 96 da mata 19 kuma sun kammala samun horon na tsawon watanni tara a Kwalejin.

Ya ce yaki da cin hanci da rashawa ba abu ne mai sauki ba, yana mai jaddada cewa yakin da gwamnatin shugaba Buhari ta yi akan cin hanci da rashawa ya fi na sauran gwamnatocin baya.

Tun da farko, yayin da yake nuna godiya ga shugaba Buhari, ya ce shugaban kasa ya karfafa hukumar a kokarinsa da kuma kishinsa na kakkabe cin hanci da rasha daga kasar nan, wadanda tasirinsu ya kawo tsaiko ga ci gaban kasar.

Leave a Reply

%d bloggers like this: