Gwamna Masari Ya Kaddamar Da Gadar Sama Ta Farko Da Gwamnatinsa Ta Gina A Katsina

0 107

Gwamnan jihar Katsina, Aminu Masari, ya kaddamar da gadar sama ta farko da gwamnatinsa ta gina akan kudi Naira Miliyan dubu 6 da Miliyan 400.

An rawaito cewa an fara aikin ginin gadar ne a watan Mayun bara.

Gwamnan ya kuma kaddamar da titin Kofar Guga zuwa Sullubawa zuwa Masanawa mai tsawon mita 900 da aka bayar a kan kudi Naira Miliyan dubu 1 da Miliyan 300.

Da yake jawabi yayin kaddamar da aikin a jiya, gwamnan ya ce an bayar da kwangilolin aikin gadar ne a wani bangare na kokarin rage cunkoso da kuma saukaka zirga-zirgar ababen hawa.

Aminu Masari ya bayyana cewa an bayar da aikin gina gadar Kofar Kwaya akan kudi naira miliyan dubu 2 da miliyan 800 sai gadara Kofar Kaura da aka bayar da aikinta akan kudi naira miliyan dubu 2 da miliyan 900.

Leave a Reply

%d bloggers like this: