Wasu Daliban Jami’ar Abubakar Tafawa Balewa (ATBU) Sun Lalata Motocin Wasu Jami’an Soji

0 68

Wasu daliban jami’ar Abubakar Tafawa Balewa (ATBU) a daren jiya Litinin sun lalata wasu motoci guda biyu na wasu jami’an soji da suka kai farmaki ga shugaban kungiyar malaman jami’o’i ta kasa (ASUU) reshen jami’ar, Dr Ibrahim Inuwa.

An rawaito cewa rikicin ya fara ne lokacin da wasu sojoji cikin motoci biyu suka so shiga harabar jami’ar amma jami’an tsaron jami’ar suka tare su a kofar shiga jami’ar saboda motocinsu na da gilashi mai duhu, wanda ya saba wa dokar jami’ar.

Da yake magana a kan lamarin, Dakta Ibrahim Inuwa ya ce yana kan hanyarsa ta komawa gida ne ya ga sojoji suna matsawa jami’in tsaron sai yaje wajen domin shiga tsakani.

Da aka tuntubi shugaban sashen yada labarai da hulda da jama’a na jami’ar ATBU, Kabiru Garba Aminu, ta wayar tarho, ya tabbatar da faruwar lamarin, inda ya ce an samu rikici tsakanin wasu sojoji da jami’an tsaron jam’ar, amma an shawo kan lamarin.

Shi ma jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar, Ahmed Wakili ya tabbatar da faruwar lamarin.

Leave a Reply

%d bloggers like this: