An Gudanar Da Bikin Ranar Kudan Zuma Ta Duniya A Jami’ar Tarayya Dake Dutse

0 72

Cibiyar kula da ilimin halittu a yankuna masu zafi ta jami’ar tarayya dake Dutse ta bi sahun sauran cibiyoyi da hukumomin domin gudanar da bikin ranar kudan zuma ta duniya wacce majalisar dinkin duniya ta ware.

Da yake magana yayin kaddamar da bikin da aka gudanar a babban dakin taron jami’ar, daraktan cibiyar, Farfesa Musa Mustapha yace an gudanar da bikin ne domin tunawa da ranar da kuma kara wayar da kan jama’a dangane da muhimmancin zuma da muhimmiyar rawar da yake takawa ga rayuwar halittu.

Ya kara da cewa kiwon zuma zai habaka tattalin arzikin jihar Jigawa da ma kasarnan baki daya, kamar yadda ke faruwa a kasashe da dama na duniya wadanda suka dogara da hakan, inda ya kara da cewa farashin ruwan zuma lita daya yafi na man fetur.

Tunda farko a jawabansu daban-daban, shugaban sashen ilimin dazuka da namun daji, Dr. Jibrin Jibo da shugaban tsangayar kimiyya, sun bukaci dalibai da suke tunani mai kyau tare da yin sana’o’in da za su tallafawa rayuwarsu bayan kammala makaranta. Yayin bikin, Dr. Danjuma Ahmad Sufi da Kasim Dele sun gabatar da makalu akan amfanin kiwon zuma ga cigaban tattalin arziki.

Leave a Reply

%d bloggers like this: