’Yan Bindiga Sun Mamaye Gundumomi a Katsina da Kauyuka 10 a Sakkwato, Mutane da Dama Sun Rasa Rayukansu
A zaman majalisar dokokin Katsina, Hon. Ibrahim Umar Dikko, babban mai tsawatarwa a majalissar jihar Katsina, ya fashe da kuka yana cewa daga cikin gundumomi 10 na Matazu da yake wakilta, guda 8 sun shiga hannun ’yan bindiga.
Ya bayyana yadda manoma ba sa iya zuwa gonakinsu saboda hare-hare, inda aka kashe akalla mutane 12 a cikin kwanaki biyu, ciki har da wani matashi da aka kashe a bakin makaranta, tare da sace shanu.
A Sakkwato, ’yan bindiga karkashin Kallamu, abokin Bello Turji sun kai farmaki a kauyuka 10 ciki har da Dan Tudu, Makuwana da Gidan Bature, inda suka kashe mutane tare da sace wasu da dama ciki har da soja ɗaya da jami’an tsaro hudu, sannan aka yi garkuwa da mutane sama da 50 tare da sace shanu fiye da 100.
Galadiman Gobir ya tabbatar da mutuwar mutane 8 a wasu kauyuka, yayin da mazauna yankin suka ce hare-haren sun kai sau 2 zuwa 3 cikin kwanaki hudu, lamarin da ya tilasta wa jama’a barin gidajensu.
Kwamishinan ’yan sandan Sakkwato, Ahmed Musa, ya tabbatar da faruwar lamarin tare da ziyarar jajantawa ga al’umma.