’Yan Bindiga Sun Sanya Wa Jama’a Harajin N40m A Sakkwato

0 89

’Yan bindiga sun sanya wa jama’a harajin N40m a Sakkwato

Al’ummar garin Kebbe da ke Ƙaramar Hukumar Kebbe a Jihar Sakkwato na cikin fargaba, bayan ’yan bindiga sun ƙaƙaba musu harajin Naira miliyan 40 tare da barazanar kai musu hari idan suka ƙi biyan kuɗin.

Rahotanni sun ce ’yan bindigar sun aike musu da saƙon ta hannun wani mazaunin garin, Abara Jaji, yayin da suka tare shi a lokacin da yake kan hanyar zuwa yin itace.

Wata majiya ta ce Jaji ya ga ’yan bindigar a kan hanya, lamarin da ya sa ya tsere ya bar babur ɗinsa.

Nan take suka bi bayansa tare da kama shi sannan suka ba shi wata waya ƙirar Tecno mai ɗauke da layi a ciki.

Sun umarce shi da ya kai wa Hakimin Kebbe ko wakilinsa wayar, tare da isar da buƙatarsu ta Naira miliyan 40.

Sun kuma yi barazanar kai wa garin hari tare da ƙone kadarorinsu idan ba a biya kuɗin ba.

Jaji, ya kai wa wakilin hakimin, Murtala Muhammad saƙon, wanda daga baya ya kai rahoton lamarin ofishin ’yan sanda.

’Yan bindigar sun sake kiran wayar yayin da Jaji da jami’an tsaro ke tattauna lamarin.

An saka wayar a lasifika, inda kowa ya ji abin da suke nema.

Kakakin Rundunar ’Yan Sandan Jihar Sakkwato, DSP Ahmad Rufai, ya ce rundunar ta sane da lamarin.

“Muna sane da lamarin kuma muna aiki a kai,” in ji shi.

Mazauna garin sun ce lamarin ya haifar da fargaba tare da rage harkokin kasuwanci, yayin da wasu mutane, musamman mata, suka fara barin garin saboda tsoro.

Wani mazaunin garin ya ce bai kamata a bai wa ’yan bindigar kuɗin ba.

“Ba ma son a ba su kuɗin, domin idan aka ba su, za su ci gaba da ƙaƙaba mana irin wannan haraji lokaci zuwa lokaci.”

Mazauna garin sun buƙaci gwamnati ta ƙara yawan jami’an tsaro a yankin domin kare garin daga hare-haren ’yan bindiga.

Barazanar na zuwa ne bayan wasu hare-hare da aka kai a Ƙaramar Hukumar Kebbe a cikin watan Agusta.

A ranar 3 ga watan Agusta, an kashe ASP Bala Wakili, wani jami’in ’yan sanda, yayin musayar wuta da ’yan bindiga, tare da ƙone motocin sintiri guda biyu.

A ranar 14 ga watan Agusta kuma, an kashe sojoji huɗu a wani hari da aka kai Kebbe, yayin da wasu mutane 34 suka rasa rayukansu a harin da aka kai ƙauyen Ungushi a ranar.

Bayan hare-haren, rundunar soji ta tura ƙarin jami’an tsaro da makamai zuwa yankin.

Leave A Reply

Your email address will not be published.