Rahotanni daga Hukumar Sadarwa ta Kasa, NCC, sun nuna cewa yawancin ‘yan Najeriya sun rage amfani da intanet bayan kara farashin sabis na sadarwa da kashi 50 cikin 100 tun farkon Janairun bana.
Alkaluma sun nuna cewa amfani da bayanan intanet ya ragu daga terabayit miliyan daya a watan Janairu zuwa terabayit dubu 893 a watan Fabrairu, raguwar da ta zo daidai da fara sabon tsarin farashin.
Duk da cewa an sami karin amfani a watan Maris zuwa terabayit dubu 995, bai kai na Janairun ba.
Farashin kira ya tashi daga naira 6.40 zuwa naira 9.60 a minti daya, yayin da sakon SMS ya tashi daga naira 4 zuwa naira 6, sai kuma 1GIG da ya hau daga naira 287 zuwa naira 431, karo na farko da aka samu irin wannan sauyi cikin sama da shekaru goma.