Yan Nigeria Shiga Damuwa Kan Batun Cire Tallafin Mai.

0 111

A halin da ake ciki, ‘yan Najeriya sun nuna damuwarsu kan matakin da gwamnatin kasar ta dauka na mayar da aikin cire tallafin man fetur ga gwamnati mai zuwa.

‘Yan kasar dai na kallon tallafin man fetur a matsayin daya daga cikin ribar da suke samu daga gwamnati, wanda suke ganin an kasa samar da sauran ababen more rayuwa kamar wutar lantarki da tsaro duk da samun biliyoyin daloli a duk shekara daga mai fetur.

Da yake zantawa da manema labarai, Barista Ken Ukaoha ya ce  Yanzu haka ‘yan Najeriya na fama da kuncin ababan more rayuwa sakamakon hauhawar farashin kayayyaki. Baya ga Farashin kayan abinci sun mamaye kasarnan kuma Karancin mai na nan daram. Farashin iskar gas da dizal sun yi tashin gwauron zabi.

 Farashin man fetur na iya kaiwa N750 kowace lita

Masu ruwa da tsaki a fannin sun shaida wa ‘yan Najeriya cewa su shirya siyan  kowace litar man fetur a gidajen mai akan Naira 750.

Da yake jawabi a wurin taron, Shugaban IPMAN na kasa, Chinedu Okoronkwo, wanda ya samu wakilcin Konturola na ayyuka na kungiyar Mike Osatuyi, ya bayyana cewa ’yan kasuwar suna ba da cikakken goyon baya ga shirin gwamnati na fara aiwatar da cikakken tsari na sassan kasan. Okoronkwo ya gargadi ‘yan Najeriya da su shirya biyan kusan Naira 750 na kowace litar man fetur bayan kammala aikin cire tallafin.

Leave a Reply

%d bloggers like this: