’Yan sanda sun kama mutum 16 kan zargin satar mutane, sun kwato kayan N69m a Kaduna
Wasu mutum 16 bisa da ake zargin masu garkuwa ne sun shiga hannun hukuma a Jihar Kaduna.
Wasu mutum uku da ake zargin masu safarar makamai ne da kuma mutum shida da ake zargin masu safarar jabun kudaden kasashen waje ne sun shiga hannun hukumar.
Rundunar ’yan sandan jihar ce ta sanar da haka tare da ta ƙwato makamai, kayayyakin sata na miliyoyin naira, dabbobi da miyagun kwayoyi a jerin samamen da ta gudanar a sassan jihar cikin makonni biyu da suka gabata.
Kwamishinan ’yan sandan jihar, Rabiu Muhammad, ne ya bayyana hakan yayin taron manema labarai a Kaduna ranar Talata.
Ya ce a cikin wannan lokaci, jami’an rundunar sun hallaka wasu fitattun masu garkuwa da mutane a wasu hare-hare daban-daban.
A cewarsa, kayayyakin da aka ƙwato sun hada da bindigogi 10, na’urorin sola guda 190 da kudinsu ya kai kimanin Naira miliyan 69, mota ɗaya da aka sace, fakiti 83 na miyagun ƙwayoyi, wayoyin hannu 32 da aka sace, talabijin guda biyu, shanu 410 da kuma takardun jabun Dalar Amurka guda 170.
Kwamishinan ya ce an samu nasarorin ne sakamakon sahihan bayanan sirri da haɗin gwiwar sauran hukumomin tsaro da ƙungiyoyin masu aikin sa-kai na tabbatar da tsaro.
Rabiu Muhammad ya ce jami’an rundunar sun kama wata budurwa mai shekara 20 mai suna Aisha Barau a ƙauyen Ramin Kura ranar 21 ga Yuli, bayan da ake zargin an kama ta tana ƙoƙarin canja takardun jabun dalolin Amurka zuwa Naira.