‘Yan Sanda Sun Kwato Babura Da Aka Sace A JIhar Jigawa

0 68

Rundunar ’Yan Sandan Jihar Jigawa ta samu nasarar kwato wasu babura guda biyu da aka sace a wasu samame da jami’anta suka gudanar a sassa daban-daban na jihar.

A Dutse, jami’an rundunar sun kama wasu mutane da ake zargi da satar babur, inda aka kwato baburin tare da mayar wa mai shi bayan gudanar da bincike.

Haka kuma a karamar hukumar Gwaram, ‘yan sanda sun kama wani mutum da ake zargi da satar wani babur, inda aka samu nasarar kwato shi kafin a kai ga sayar da shi.

Rundunar ta bayyana cewa ana ci gaba da bincike kan lamarin, yayin da aka gurfanar da wasu daga cikin wadanda ake zargi a gaban kotu.

Kwamishinan ’Yan Sandan Jihar Jigawa, Haruna A. Yahaya, ya yaba wa jami’an rundunar bisa kokarinsu wajen yaki da masu aikata laifuffuka tare da kira ga jama’a su ci gaba da bai wa jami’an tsaro hadin kai da bayanan sirri.

Leave a Reply