

Rundunar ‘yan sandan jihar Jigawa ta kama wasu mashahuran masu safarar miyagun kwayoyi su hudu a wani samame da aka kai zuwa maboyar bata gari a masarautun Hadejia da Kazaure.
Kakakin rundunar, ASP Lawan Shiisu Adam ya tabbatar da kamen a wata sanarwa da ya rabawa manema labarai yau a Dutse.
Ya ce kamen ya biyo bayan umarnin kwamishinan ‘yan sandan jihar ne na kakkabe maboyar masu aikata miyagun laifuka a fadin jihar.
A cewar sanarwar, an kama wasu dilolin miyagun kwayoyi su biyu a jiya, yayin da aka kai wani samame zuwa wajen da ake zargin maboyarsu ce a kasuwar Malam Madori, bayan samun bayanan sirri.
Ya kara da cewa an damke sauran dilolin miyagun kwayoyin su biyu a Kofar Tasha dake karamar hukumar Kazaure.
Ya ce za a gurfanar da wadanda ake zargin a gaban kotu bayan kammala bincike.