An gano gawarwaki sama da 50 bayan harin da aka kai wasu a jihar Zamfara

0 36

A halin da ake ciki, mazauna kananan hukumomin Anka da Bukkuyum a jihar Zamfara sun ce sun gano gawarwaki sama da 50 bayan harin da aka kai a farkon makon nan a wasu kauyukan jihar.

Mazauna yankin sun kuma ce har yanzu ana ci gaba da gudanar da bincike domin gano wasu gawarwaki da wadanda suka samu rauni.

Gidan Radion Sawaba ya bayar da labarin yadda ‘yan bindiga suka kone kauyukan jihar Zamfara guda biyar.

Wani dan siyasa a yankin mai suna Hamza Adamu ya shaidawa manema labarai cewa shugaban kungiyar ‘yan banga na karamar hukumar Anka, Gambo Abare na daya daga cikin wadanda aka kashe.

Wani Murtala Waramu, da ya sha dakyar a harin wanda har yanzu yake cigaba da neman ‘ya’uwansa, ya shaida wa Muryar Amurka cewa kawo yanzu an gano gawarwaki 58.

Ya ce akwai kauyuka da dama da ba a bincika ba, amma ya ce a galibin kauyukan da suka ziyarta, ‘yan fashin dajin sun kone gidaje da shaguna.

Leave a Reply

%d bloggers like this: