Gwamnatin jihar Jigawa ta dauki mutum 1000 aiki domin cike guraben aiki

0 138

Gwamnatin jihar Jigawa ta dauki mutane fiye da dubu daya aiki domin cike guraben aikin gwamnati a shekarar data gabata.

Shugaban ma’aikata na jiha, Alhaji Hussaini Ali Kila ne ya bayyana haka lokacin da yake tilawar nasarorin da ofishin sa ya samu a shekarar ta 2021 ta cikin shirin Gidan Radion Jigawa na musamman.

Ya ce an dauki daliban da suka sami shedar digiri mafi daraja karkashin tsarin gwamnati na daukar aiki kai tsaye da kuma bangaren kiwon lafiya dana ilimi.

Alhaji Hussaini Ali Kila ya cigaba da cewa an yiwa ma’aikata da dama karin girma, kari akan basu horo da sake horas dasu domin samun kwarewa wajen gudanar da ayyukansu.

Shugaban ma’aikatan ya kuma yabawa kudirin gwamnatin jiha na biyan albashi da fansho da kuma hakkokin ma’aikatan da suka bar aiki akan lokaci.

Daga nan ya yi kira ga ma’aikata su kara kokari wajen gudanar da ayyukansu, tare da gargadin cewa gwamnati ba zata amince da kin zuwa wurin aiki ko fashi ba.

Leave a Reply

%d bloggers like this: