‘Yan sandan jihar Neja sun kama tsohon soja da aka kora daga aiki bisa zargin yin damfara da sunan soja
Rundunar ‘yan sandan jihar Neja ta kama wani tsohon soja da aka kora daga aiki, Michael Musa, bisa zargin sa dayin damfara da sunan soja a kan masu sana’ar POS.
Kakakin ‘yan sandan jihar, Wasiu Abiodun, ya ce wanda ake zargin ya rika sanya kayan soja yana yaudarar mutane don karɓar kuɗi ba bisa ƙa’ida ba.
Daga cikin waɗanda ya yaudara akwai wani a Bida da ya rasa Naira dubu 120, da wani a Kataeregi da ya yi asarar dubu 300, da kuma wani a Minna da aka yaudare shi da Naira dubu 50.
Bayan kama shi, Musa ya amsa laifinsa, yayin da ‘yan sanda ke ci gaba da bincike, inda ake samun ƙarin koke-koke daga sabbin waɗanda ya damfara.