’Yan takarar Gwamnan Gombe a PDP sun yi fatali da batun shigar Pantami

0 153

Manema takarar gwamnan Jihar Gombe a ƙarƙashin jam’iyyar PDP sun yi fatali da jita-jitar da ke cewa tsohon Ministan Sadarwa, Isa Ali Pantami, na shirin shiga jam’iyyar domin neman takarar gwamna.

Jita-jitar ta fara yawo ne bayan zaɓen fidda gwani na jam’iyyar APC da aka gudanar a ranar 21 ga watan Mayun 2026.

A wata sanarwar haɗin gwiwa da suka fitar a ranar Asabar, manema takarar gwamnan na PDP sun bayyana cewa babu wata tattaunawa ko matakin da aka ɗauka dangane da shigar Pantami cikin tsarin jam’iyyar.

Sun kuma jaddada cewa PDP a jihar za ta ci gaba da tafiya bisa tsarin jam’iyya da kuma matakan da shugabanninta suka amince da su, ba tare da nuna son kai ga wani ɗan takara ba.

Maneman takarar sun buƙaci magoya bayan jam’iyyar da su yi watsi da rahotannin da ke yawo, suna masu cewa jam’iyyar za ta ci gaba da aiki domin tabbatar da haɗin kai da kuma shirye-shiryen tunkarar zaɓen 2027.

Leave a Reply