‘Yansanda a jihar Imo sun tarwatsa wani mummunan hari daga ‘yan kungiyar masu fafatukar kafa kasar Biafar ta IPOB da aka haramta

0 30

‘Yansanda a jihar Imo a yau sun tarwatsa wani mummunan hari daga ‘yan kungiyar masu fafatukar kafa kasar Biafar ta IPOB da aka haramta.

Harin na yau shine na biyar da aka kai kan ofisoshin ‘yansanda a jihar.

Kakakin ‘yansanda na jihar, Michael Abattam, cikin wata sanarwa da ya fitar a yau yace ana zargin ‘yan kungiyar masu fafatukar kafa kasar Biafar ta IPOB da aka haramta ne suka kai hari kan ofishin ‘yansanda na Mbieri.

Michael Abattam yace ‘yan bindigar sun yi amfani da abubuwan fashewa, inda ya kara da cewa abubuwan fashewar sun yi ta’adi kadan akan wasu motoci da tagogin ofishin.

Kakakin ‘yansandan yace mukaddashin kwamishinan ‘yansanda na jihar, Maman Giwa, ya bukaci mazauna jihar da su cigaba da bayar da hadin kai da goyon baya ga yaki da rashin tsaro ta hanyar bawa hukumomin tsaro, musamman ‘yansanda, sahihan bayanai domin daukar matakin gaggawa.

Yace rundunar ta fara bincike kan lamarin kuma ana kokarin kama wadanda ake zargin da suka arce.

Leave a Reply

%d bloggers like this: