Yawan wadanda suka mutu a ambaliyar ruwan wannan makon a kasar Afghanistan sun karu zuwa akalla 113

0 74

Yawan wadanda suka mutu a ambaliyar ruwan wannan makon a lardin Nuristan na gabashin kasar Afghanistan sun karu zuwa akalla 113, kuma gomman mutane sun bata.

Ana cigaba da aikin ceto, kwanaki bayan mamakon ruwan sama kamar da bakin kwarya ya mamaye gundumar Kamdesh a lardin da Talaban ke iko da shi, mai nisan kimanin kilomita 200, arewa maso gabashin babban birnin kasar, Kabul, a ranar Laraba.

Mai magana da yawun hukumar kula da annoba ta kasar Afghanistan, Abdul Samai Zarbi, ya shaidawa manema labarai cewa sama da gidaje 170 ne suka lalace, inda suka shafi kimanin iyalai 300.

Bayan cewa adadin wadanda suka jikkata sun kai 34, Abdul Zarbi yayi nuni da cewa adadin na farko kuma suna iya canjawa.

Ambaliyar ruwan ta kuma lalata wata muhimmiyar gada a gundumar, a cewar hukumar kula da annobar, wacce tace hakan ya sanya bata iya isar da kayan bukata irinsu abinci da tantunan wucin gadi da magunguna ga wadanda lamarin ya shafa.

Leave a Reply

%d bloggers like this: