Hukumar lafiya ta jihar Jigawa tana sa ran yiwa yara miliyan 1 da dubu 700 allurar rigakafin polio

0 89

Hukumar lafiya matakin farko ta jihar Jigawa tace tana sa ran yiwa yara miliyan 1 da dubu 700 allurar rigakafin polio a zagaye na biyu na rigakafin a jiharnan.

Sakataren zartarwar hukumar, Dr Kabir Ibrahim, ya gayawa manema labarai a jiya cewa an aika da isassun ma’aikata domin gudanar da aikin a fadin jiharnan.

Kabir Ibrahim yace manufar da aka sanya a gaba ita ce tabbatar da cewa an yiwa dukkan yara ‘yan kasa da shekara 5 allurar rigakafin.

Yace hukumar ta karbi alluran rigakafin domin tabbatar da aikin kamar yadda ya kamata.

Sakataren, wanda ya nemi hadin kai da goyon bayan al’umma da shugabannin addinai da sauran masu ruwa da tsaki wajen gudanar da aikin, ya bukaci iyaye su kai ‘ya’yansu domin rigakafin a guraren da aka ware.

Leave a Reply

%d bloggers like this: