An dage zaben kananan hukumomin jihar Kaduna zuwa ranar 4 ga watan Satumba

0 99

A wani labarin kuma, shugabar hukumar zabe mai zaman kanta ta jihar Kaduna, Dr Saratu Dikko Audu, ta sanar da dage zaben kananan hukumomin jihar zuwa ranar 4 ga watan Satumbar 2021.

Ta sanar da haka a helkwatar hukumar lokacin da take jawabi ga masu ruwa da tsaki yau a Kaduna.

Tun da farko an tsara gudanar da zaben shugabannin kananan hukumomi da kamsiloli a dukkanin kananan hukumomi 23 na jihar Kaduna, a ranar Asabar, 5 ga watan Yuni, kafin daga bisani a dage zaben zuwa ranar 14 ga watan Augusta.

Wannan shine karo na uku da aka dage gudanar da zaben.

Leave a Reply

%d bloggers like this: