DSS ta fitar da mutanen da ta kama a gidan dan fafutukar kafa kasar yarbawa, Sunday Igboho

0 94

Hukumar tsaro ta farin kaya (DSS) ta fitar da mutanen da ta kama a gidan dan fafutukar kafa kasar yarbawa, Sunday Adeyemo, wanda aka fi sani da Igboho, a jihar Oyo, a kotu a yau.

An gabatar da wadanda aka tsare a gaban babbar kotun tarayya da ke Abuja, biyo bayan umarnin mai shari’ah Obiora Egwuatu, wanda ya tursasawa hukumar ta DSS ta fito da wadanda ake zargin.

Hukumar ta DSS a baya ta take umarnin kotu da alkalin ya bayar a ranar 23 ga watan Yuli na gabatar da wadanda aka tsare a gaban kotu a ranar 29 ga watan Yuli.

Igboho na fuskantar shari’ah a jamhuriyar Benin bayan kamen da aka yi masa a kasar a watan da ya gabata.

Leave a Reply

%d bloggers like this: