Anyi hasashen samun karuwa kashi 5 cikin 100 na kudaden shiga ta hanyar sabon shirin rijistar ababen hawa na kasa

0 87

Ma’aikatar Kudi, Kasafin Kudi da Tsare-Tsaren Kasa ta yi hasashen samun karuwa kashi 5 cikin 100 na kudaden shigar kasarnan ta hanyar sabon shirin rijistar ababen hawa na kasa.

Daraktan labarai na ma’aikatar, Charles Nwodo, ya sanar da haka a wajen taron wayar da kai da aka shirya a Lagos a karshen mako.

Yace karkashin sabon shirin rijistar ababen hawa na kasa, akwai cikakke bayanin tarihin ababen hawa dake bin titunan kasarnan, wanda zai taimakawa hukumomin tsaro gano ababen hawan da aka sace.

Ma’aikatar da hukumar hana fasa kwauri ta kasa (kwastan) a watan Afrilu suka fitar da shirin kirkirar kudin bayanai domin ababen hawan da aka shigo dasu cikin kasa, da niyyar dakile masu kauracewa biyan kudin fito da sata.

Kwamishinan sufuri na jihar Lagos, Frederick Oladeinde yace kimanin ababen hawa miliyan 3 ne suke bin titunan jihar, kuma ana aikata laifuka dayawa ta hanyar amfani da ababen hawan.

Leave a Reply

%d bloggers like this: