Gwamna Zulum ya sanya ido wajen rabon tallafin kayan abinci ga yan gudun hijira

0 84

Gwamnan jihar Borno, Babagana Umara Zulum, a jiya ya sanya ido wajen rabon tallafin kayan abinci ga yan gudun hijirar da suka dawo a kauyen Garade, dake yankin karamar hukumar Marte.

Garin Marte na daya daga cikin garuruwan da mayakan ke da iko sosai, wanda mazauna garin suka gudu suka bar shi, kafin daga bisani sojojin Najeriya da gamayyar hukumomin tsaro su ceto shi.

Mazauna garin da aka kora sun fara komawa garin Marte daga Dikwa, Moguno da Maiduguri a ranar 30 ga watan Nuwamban 2020.

Jumillar ‘yan gudun hijira dubu 2 da 870 da suka koma, daga gidaje 500, suka zama rukunin farko na wadanda suka koma suka samu matsuguni a unguwar hukumar raya tafkin chadi da aka gyara, bayan gwamnatin jihar ta mika bukatar ga manajin daraktan hukumar.

Leave a Reply

%d bloggers like this: