An gudanar da aikin yashe Kogi mai nisan kilomita 95 a Guri da Kirikasamma

0 85

Gwamnatin jihar Jigawa da hadin gwiwar gwamnatin tarayya sun gudanar da aikin yashe Kogi mai nisan kilomita 95 a yankunan kananan hukumomin Guri da Kirikasamma.

Mai baiwa gwamna shawara kan shigo da alumma cikin harkokin gwamnati Alhaji Hamza Muhammad Hadejia ya sanar da hakan ta cikin wani shirin radio Jigawa.

Yace baya ga haka an yashe kogi na tsawon kilomita 35 a mahadar Kogin Hadejia da Kafin Hausa dake tsakanin Miga da Kafin Hausa da nufin bude kogin domin samarwa da ruwa hanyar wucewa.

Hamza Hadejia ya kara da cewar baya ga aikin yashe kogi ana gudanar da aikin jinga na gefe da gefe a wurare da dama domin dakile ambaliyar ruwa.

Mai baiwa gwamnan shawara ya kara da cewar kananan hukumomi 22 ne ke fuskantar barazanar ambaliyar ruwa a jihar nan kuma gwamnatin jiha na daukar matakan gaggawa domin dakile ambaliyar ruwan a bana.

Leave a Reply

%d bloggers like this: