Garba Shehu ya kalubalanci Sule Lamido

0 128

Babban mataimaki na musamman ga shugaban kasa kan harkokin yada labarai, Malam Garba Shehu, ya kalubalanci tsohon gwamnan jihar Jigawa Sule Lamido da ya fito ya yi bayani kan yadda tsohon gwamna Saminu Turaki ya mika masa tikitin takarar gwamna a 2007 kuma ya yi masa yakin neman zabe.

Garba Shehu ya mayar da martani ne kan kalaman Sule Lamido wanda ya caccaki Shugaban Kasa Muhammadu Buhari saboda karbar wadanda suka sauya sheka a Fadar Shugaban Kasa dake Abuja.

Sule Lamido ya bayyana hakan a matsayin wani nau’in cin hanci da rashawa da ya shafi sace nasarar zaben jam’iyya.

Garba Shehu ya ce shugaba Buhari ya zama Shugaban kasa ta hanyar zama dan jam’iyyar siyasa kamar yadda Kundin Tsarin Mulki ya tanadar. Yayin da yake watsi da ra’ayin cewa karbar masu sauya shekar wani nau’in cin hanci da rashawa ne, Garba Shehu ya shaidawa tsohon gwamnan na jihar Jigawa cewa APC ba za ta yi koyi da al’adun jam’iyyar PDP ba wacce ke sanya hukumar hana cin hanci da rashawa ta hana ‘yan takara, takara kuma fadar shugaban kasa ta goyi bayan tsige gwamnoni ba bisa ka’ida ba.

Leave a Reply

%d bloggers like this: