Farfesa Attahiru Jega ya yi kira ga ‘yan ƙasar su dawo daga rakiyar manyan jam’iyyu na APC da PDP

0 158

Tsohon Shugaban Hukumar Zaɓen Najeriya, Farfesa Attahiru Muhammad Jega, ya yi kira ga ‘yan ƙasar su dawo daga rakiyar manyan jam’iyyu na APC da PDP, saboda yadda suka kasa taɓuka wani abun arziƙi a tsawon shekara 20 da suka shafe suna mulki.

Yayin wata hira ta musamman da BBC Hausa, Jega ya ce muguwar rawar da jam’iyyun biyu suka taka a tsawon waɗannan shekaru ta nuna ƙarara cewa babu buƙatar a sake yin amanna da su a kan cewa za ta sauya zani idan aka sake ba su wata dama a nan gaba.

Tsohon shugaban na INEC ya kara da cewa rashin shugabanci na gari ne ya haifar da dukkan matsalolin da Najeriya ke fama da su, har ta kai ga wasu na neman a raba kasar a halin da ake ciki.

Leave a Reply

%d bloggers like this: