Najeriya ta karbi kunshin alluran rigakafin Korona na kamfanin Moderna guda miliyan 4

0 71

Najeriya ta karbi kunshin alluran rigakafin annobar Korona na kamfanin Moderna  guda miliyan 4  daga Amurka, a yayin da kasar ke kara azama wajen kokarin dakile yaduwar cutar da ta sake kunno kai  a karo na 3.

Jami’a daga ofishin asusun kula da kananan yara na duniya a Najeriya  suka karbi wadannan alluran da suka isa kasar cikin jiragen sama guda 2, a filin tashi da saukan jiragen sama na Abuja.

Wannan ne karo na biyu da alluran rigakafin wannan shu’umin cuta ke isowa kasar da ta fi yawan al’umma a nahiyar Afrika.

Leave a Reply

%d bloggers like this: