‘Ya’yan Marigayi Manjo Rabe Sun Musanta Labarin Sakin Mahaifiyarsu, Sun Bayyana Musabbabin Mutuwarsa

0 119

‘Ya’yan marigayi Manjo Rabe Abubakar sun musanta rahotannin da ke cewa an saki mahaifiyarsu daga hannun masu garkuwa da mutane.

Ɗaya daga cikin ‘ya’yan marigayin, Ishak Rabe Abubakar, ya bayyana cewa har yanzu mahaifiyarsu na hannun masu garkuwar, yana mai cewa suna ci gaba da jiran matakin da mahukuntan Najeriya za su ɗauka domin ganin an kuɓutar da ita.

Ishak ya kuma ƙaryata bayanin da gwamnatin Jihar Katsina ta bayar a baya cewa mahaifinsa ya rasu ne sakamakon ciwon sukari ko hawan jini.

A cewarsa, marigayi Manjo Rabe Abubakar ya rasu ne bayan da maciji ya sare shi a lokacin da yake tsare a hannun masu garkuwa da mutane.

Ya ce iyalan marigayin na ci gaba da fatan ganin an ceto mahaifiyarsu cikin ƙoshin lafiya, tare da kira ga hukumomin tsaro da gwamnati su ƙara ƙaimi wajen tabbatar da an kuɓutar da ita.

Leave a Reply