Za’a Binne Gawarwaki 49 Wanda Ba’a Tantance Suwaye Ba A Chikun Ta Jihar Kaduna

0 78

Majalisar Karamar Hukumar Chikun ta Jihar Kaduna ta bayyana kudirinta na binne gawarwaki 49 wadanda ba a tantance ba, wanda aka ajiye a dakin ajiyar gawa na babban asibitin Sabon Tasha, mako da yagabata.

Shugaban karamar hukumar, Salasi Nuhu Musa, wanda ya bayyana hakan jiya a Kaduna, ya ce jami’an ‘yan sanda daga sashin Toll Gate da kuma ofishin ‘yan sanda na Kasuwan Magani sun ajiye gawarwakin a lokuta daban-daban.

Ya ce, an bayyana sunayen gawarwakin guda 25 daga cikin 49, yayin da sauran 24 ba a iya tantance su ba, saboda ba za’a iya tantancewa a lokacin da aka ajiye gawarwakin a dakin ajiyar gawa.

Majalisar karamar hukumar Chikun ta samu amincewar ma’aikatar lafiya ta jihar Kaduna da ma’aikatar harkokin kananan hukumomi domin gudanar da jana’izar wasu gawarwaki 49 da ba a san ko su waye ba.

Leave a Reply

%d bloggers like this: