Za’a Sanya Na Mujiya Ga Jami’an Kwastam – Hameed Ali

0 114

Shugaban hukumar Kwastan ta Kasa, Kanal Hameed Ali Mai Ritaya, ya kaddamar da  Yansandan Kwastan wanda zasu dinga sanya ido da tsawatarwa ga Jami’an Kwastan.

Da ya ke  jawabi yayin kaddamarwar, Hameed Ali, ya ce kwao gyara ga hukumar ta Kwastan na daga cikin dalilan da Shugaba Muhammadu Buhari ya nada shi a matsayin shugaban hukumar domin ciyar da ita ga ba tare da yin aiki kamar yadda ya kamata.

Daga nan sai ya umarci Jami’an na yansandan kwastan, da suyi aiki tukuru kamar yadda dokokin aiki na hukumar suka tanadar, inda ya hore su, da suyi aiki ba tare da nuna bam-bamci ba ga kananan ma’aikata ko manya ba.

Inda ya kara da cewa sabon sashen na yansandan kwastan, na da damar kama tare da tsare da kuma hukunta duk wani Jami’in da aka kama da laifuka, ya kara da cewa hakkinsu ne kiyaye aikata laifuka.

Hameed Ali ya ce kafa sabon sashen na yansandan kwastan, zai taimaka wajen tafikar da hukumar yadda ya kamata.

Da ya ke maida Jawabi sabon shugaban sashen yan sandan, Kwanturola Muhammad Hassan ya yi alkawarin yin aiki tukuru kamar yadda aka umarcesu domin ganin sun cimma nasara.

Leave a Reply

%d bloggers like this: