

- Anyi hasashen samun ruwan sama hade da tsawa a fadin kasarnan daga yau zuwa ranar Laraba - August 23, 2021
- Wata kungiyar adawa ta ce tana da dubban mayaka da zasu fafata yaki da yan Taliban a Afghanistan - August 23, 2021
- ‘Yan bindiga sun kashe mutane 4 tare da sace wasu 50 a karamar hukumar Maradun ta jihar Zamfara - August 23, 2021
Majalisar wakilai ta kasa ta amincewa Shugaban Muhammadu Buhari da ya dana sabbin masu bashi shawara guda 15 kamar yadda tsarin mulkin kasa ya tanadar masa.
Amincewar ta biyo bayan kudirin goyan baya wanda dan majalisa wakilai Garba Ado daga Kano ya gabatar.
Amincewar na daga cikin kundin tsarin mulki a sashe na 151 da 1 cikin baka na kundin tsarin mulkin kasa.
Kundin tsarin mulkin kasa dai ya bawa shugaban kasa dama da yanada wanda yake so a matsayin mai bashi shawara domin taimaka masa a fanin gudanar da mulki.
Kamfanin Dillanci Labarai na Kasa, ya rawaito cewa Shugaba Buhari ya mika bukatar ga majalisar wakilai ta kasa inda ya ke bukatar su amince masa ya nada mutane 15 a matsayin masu bashi shawara.
Majalisar ta ce kundin tsarin mulkin kasa ya bata damar duba yawan wadanda za’a nada a matsayin masu bada shawara tare da duba albashin su da alawus-alawus.
A karshe majalisar zata tura sunayen yan majalisar ga majalisar dattijai domin neman amincewarta.