Sufeto Janar na Yansanda, Mohammed Adamu, ya jaddada alkawarinsa na yin garanbawul ga tawagar yansanda masu yaki da fashi da mamaki, da sauran bangarorin yansanda na musamman.
Sufeto Janar ya sanar da haka jiya a Abuja lokacin da ministan matasa da wasanni, Sunday Dare, ya kai masa ziyarar ban girma.
Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa ta hannun kakakin yansanda, Frank Mba.
- Airtel ta dakatar da bayar da bashin kati da data a Najeriya
- ’Yan adawa ba su isa su razanar da ni ba – Tinubu
- Sojoji sun kama masu satar man fetur a Legas, sun kama mutum 14
- Talauci ya ragu daga kaso 91 zuwa 41 a jihar Sokoto
- Bayan shekaru 12 da sace ɗaliban Chibok 272, har yanzu ba a san makomar 83 ba
Sufeto Janar yayi kira ga ‘yan kasa da suyi hakuri, inda yayi nuni da cewa ana cigaba da yin garanbawul ga tawagar yansanda masu yaki da fashi da mamaki.

Ya jaddada cewa an kama wasu daga cikin jami’an yansandan da laifin wuce gona da iri akan yan kasa, musamman matasa, kuma tuni suka fara fuskantar hukunci.
Da yake mayar da jawabi, Sunday Dare ya yabawa Sufeto Janar bisa matakin da ya dauka na gaggawa wajen magance matsalar, inda ya nemi inganta hadin gwiwa da kyakykyawar fahimtar juna tsakanin yansanda da matasa.