Zaman gida daram ga daliban Jami’o’i a Nijeria

0 126

Akwai alamu sosai dake nuna cewa daliban jami’o’in gwamnati a kasarnan za su cigaba da zama a gida kasancewar kungiyar malaman jami’o’i (ASUU) ta yi watsi da umarnin gwamnatin tarayya na cewa dukkan makarantu a kasarnan su koma bakin aiki a ranar Litinin mai zuwa.

Shugaban kungiyar ta ASUU na kasa, Farfesa Biodun Ogunyemi, a wata ganawa ta wayar tarho tare da manema labarai, yace gwamnatin tarayya bada gaske take ba dangane da tattaunawarta da kungiyar, inda ya kara da cewa lakcarori baza su koma aiki cikin yunwa ba.

Biodun Ogunyemi musamman ya caccaki Babban Akawu na Tarayya, Ahmed Idris, saboda take umarnin da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bashi na biyan malaman jami’o’i albashi.

Yayi tsokacin cewa yan Najeriya su shirya fuskantar dogon yajin aiki a jami’o’i, bisa la’akari da yadda gwamnati ke yiwa tattaunawa tsakaninsu rikon sakainar kashi.

Leave a Reply

%d bloggers like this: