Ƴan bindiga sun sace wata dattijuwa mai shekaru 70 kuma mahaifiyar shugaban ma’aikatan gwamnan jihar Kogi
‘Yan bindiga sun sace wata dattijuwa mai shekaru 70, mahaifiyar Abdulkarim Asuku, shugaban ma’aikatan gwamnan jihar Kogi.
‘Yan bindiga sun dauke dattijuwar a gidanta dake garin Nagazi a yankin karamar hukumar Adavi ta jihar.
Wani shaidar gani da ido, wanda ya nemi a sakaye sunansa, yace dattijuwar na sallar Isha’i lokacin da barayin suka shiga gidanta ta cikin masallaci, suka sace ta.
Majiyar tace barayin wadanda ke sanya da bakaken kaya, sun yi biris da magiyar dattijuwar na su kyaleta ta dauki maganinta.
Majiyar ta kara da cewa ‘yan bindigar sun tafi da ita zuwa wata mota da suke ajiye a wajen harabar gidan, kuma suka gudu da ita.
Kakakin yansanda na jihar Kogi, Williams Aya, ya tabbatar da aukuwar lamarin ga kamfanin dillancin labarai na kasa a jiya, inda yace wata tawaga karkashin jagorancin kwamishinan yansanda, Idrisu Dabban, ta tafi zuwa wajen.