Ƙungiyar farar hula a Kano sun buƙaci dakatarwa da gurfanar da jami’an gwamnati da aka zarga da hannu a badaƙalar rashawa da ta kai biliyoyin Naira.

0 648

Ƙungiyoyin farar hula (CSOs) a Kano sun buƙaci a gaggauta dakatarwa da gurfanar da jami’an gwamnati da aka zarga da hannu a badaƙalar rashawa da ta kai biliyoyin Naira.

Wannan kiran ya biyo bayan rahotannin da suka nuna cewa Daraktan sashin huldar fadar Gwamnati, Abdullahi Ibrahim Rogo, ya karkatar da Naira biliyan 6.5 tsakanin Nuwamba 2023 da Fabrairu 2025 ta hannun kamfanoni daban-daban ta hanyar kwangilolin bogi.

Haka kuma, hukumar ICPC ta kammala bincike a wata badaƙalar Naira biliyan 1.02 da ya shafi Shugaban hukumar Zaɓe ta jihar Kano (KANSIEC), Farfesa Sani Lawan Malumfashi, Sakataren hukumar Anas Mustapha, da Darakta Ado Garba, inda suka fitar da kuɗi daga asusun hukumar zuwa kamfani mai zaman kansa duk da cewa an biya ma’aikatan wucin gadi ta hanyar bankuna.

Ƙungiyoyin sun buƙaci a gurfanar da duk wadanda aka zarga, a gudanar da bincike na musamman kan dukkan ma’aikatu da hukumomin jiha, a ƙarfafa rawar majalisar dokoki wajen sa ido, da kuma samar da kariya ga masu fallasa gaskiya.

Haka zalika, sun buƙaci kafa dandalin tattaunawa da NGOs da shugabannin al’umma don ƙarfafa mulkin da zai mayar da hankali ga jama’a.

Leave a Reply