NIMET ta yi gargaɗin samun ambaliya a jihohi 19 da ke Najeriya,sakamakon yadda ake samun ruwan sama a baya bayan nan.
A baya-bayan nan ne hukumar hasashen yanayi ta kasa NIMET ta yi gargaɗin samun ambaliya a wasu jihohi 19 da ke ƙasar, sakamakon yadda ake samun mamakon ruwan sama a baya bayan nan.
Jihar Borno da aka samu mummunar ambaliya a bara, na cikin jihohin da a yanzu ma ake hasashen za a iya samun ambaliyar.
Mahukunta a jihar na cewa tuni suka fara daukar matakan da suka kamata, don kaucewa faruwar hakan.
Sai dai domin fuskantar matsalar, mutane da dama a garin sun tashi tsaye wajen gudanar da ayyukan gayya musamman wajen buɗe magudanar ruwa da sauran su.
Malam Musa Ibrahim Gilabo ya shaida wa BBC cewa sun tara kuɗi domin gudanar da ayyukan gayya a unguwarsu, sannan ya yi kira ga sauran jama’a su tahi tsaye ba sai sun jira gwamnati ba.
A nasa ɓangaren, Abdullahi Yusuf Bukar ya ce suna buƙatar gwamnati ta ƙara ƙaimi, domin a cewarsa, ya kamata gwamnati ta ware wuraren zubar da shara da kwashewa.
A zantawar BBC da gwamnan jihar, Babagana Umara Zulum ya ce ya ziyarci tushen matsalar, inda ya ce, “suna neman kariya daga Allah, amma a kwnanan nan ya je madatsun ruwan da kansa, kuma tuni ake ta aikin buɗe hanyayoyi da za a iya karkatar da ruwan domin kiyaye aukuwar ambaliyar.”